Faransa

Kotu ta tabbatar da sahihancin kundin Jam’iyyar Macron

Emmanuel Macron, shugaban Faransa
Emmanuel Macron, shugaban Faransa REUTERS/Charly Triballeau/Pool

Kotu a Faransa ta tabbatar da sahihancin zaben kundin tsarin tafiyar da jam’iyar La République en marche, ta shugaban kasar Emanuel Macron da wasu ‘ya’yan jam’iyar suka kalubalanta a gabanta.

Talla

Babbar kotun da ke Paris ta ce zaben cikin gidan da jam’iyar shugaba Macron ta La République en marche ta gudanar a ranar 23 zuwa 30 na Yuli, domin samar wa kanta dokokin tafiyar da ayyukan ya yi dai dai.

Bisa korafin rashin mutunta tsarin demokradiya a cikin jam’iyar ne, wasu daga cikin mambobinta suka bukaci soke zaben kundin da suka ce an tsara ba a kan ka’ida ba.

Mambobin da ke korafin na zargin jam’iyar ne da rasin mutunta wa’adin wata guda tsakanin aika gayyatar mambobin da kuma gudanar da zaben amincewa da kundin tafiyar da ayukan jam ‘iyar.

An kafa Jam’iyyar Macron ne a ranar 6 ga watanAfriln 2016, a lokacin da ya ke rike da mukamin ministan tattalin arziki, inda daga bisani bayan kai shi ga nasarar zama shugaban kasa, ta shiga matakin sake fasalta kanta ta fannin dokoki da kuma sauya suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.