Faransa

Macron zai dakatar da shirin kafa ofishin matarsa

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da matarsa Brigitte a fadar gwamnatin kasar ta Elysee
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da matarsa Brigitte a fadar gwamnatin kasar ta Elysee REUTERS/Thibault Camus/Pool

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na shirin janye kudirinsa na kafa ofishin matar shugaban kasa, sakamakon sukar da shirin ya gamu da shi daga bangaren ‘yan adawa da wasu mutanen kasar. A lokacin yakin neman zabensa, Macron ya yi alkawarin kafa ofishi ga uwargidansa Brigitte Macron, wacce tsohuwar malamar makaranta ce.

Talla

Siyasar kafa ofishin matar shugaban kasa ta kasance abin da ya sanya Macron a gaba a ‘yan kwananki nan, bayan takardar korafe-korafe da mutane sama da dubu 270 suka sanya wa hannu don nuna adawarsu, kana kuri’ar jin ra’ayi jama’a ta tabbatar da cewa akasarin Faransawa ba sa na’am da wannan tsari.

Fadar gwamnatin kasar ta ce, a cikin kwananki kadan masu zuwa za ta bayyana matsayin Brigitte tare da bada tabbacin cewa ba za a aiwatar da sauyi kan kundin tsarin mulkin kasar ba saboda wannan bukata.

Sai dai za a bayyana hanyoyin da Brigitte za rika samun kudadade don bukatunta.

Daya daga cikin ‘yan Majalisun Dokokin da ya fito daga jam’iyyar Macron ta Republican on the Move, Aurore Berge ya ce, bukatar Faransawa ita ce sanin adaddin kudin da ofshin matar shugaban kasar zai ci.

Ana dai ganin Faransa na son kwaikwayar tsarin Amurka ne da ke ware wa matar shugaban kasa ofishinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.