Holland

Gurbataccen kwai ya watsu a Nahiyar Turai

Holland dai na matsayin kasa ja gaba a duniya wajen kasuwanci dama sarrafa kwai inda ta ke da manyan gidajen gonar da ke aikin samar da kwai don rarraba su zuwa sassan duniya
Holland dai na matsayin kasa ja gaba a duniya wajen kasuwanci dama sarrafa kwai inda ta ke da manyan gidajen gonar da ke aikin samar da kwai don rarraba su zuwa sassan duniya Reuters

Belgium ta yi ikirarin cewa kasar Holland na da masaniyar samun sinadarin fipronil a tarin kwan da ta ke fitarwa daga gidajen gonarta zuwa sassan kasashen Turai tun a watan Nuwamban bara watanni 9 kafin gano hakan a tarayyar Turai.

Talla

Ministan albarkatun gona a kasar ta Belgium Denis Ducarme ya shaidawa majalisar dokokin kasar a yau Laraba cewa, hukumar kula da abinci ta kasar ta samu wasu bayanai da suka tabbatar da masaniyar Holland kan samuwar kwan mai sinadarin Fipronil tun a karshen watan Nuwamban bara, amma hakan bai hana ta ci gaba da fitar da kwan zuwa sassan duniya ba, la’akari da zamowar ja gaba a harkar fitar da kwai a duniya.

A cewar ministan duk da babu wata tattaunawa da suka yi a hukumance da kasar ta Holland amma ya tattauna da takwarorinsa na kasashen turai dangane da batun samuwar kwan dama lokacin da aka same shi.

Tun a ranar 1 ga Agustan da muke ne dai aka bankado batun fitar da kwan mai dauke da sinadarin Fipronil me illah ga lafiyar dan adam a kasashen Turai, lamarin daya sa Holland ta yi umarnin fitar da kwayayen dake shagunan sayarwa tare kuma da hana yin amfani da su.

Haka kuma tuni ta yi umarnin kulle kimanin manyan gidajen gona 138 tare da ware miliyoyin kajin don gujewa amfani da su.

Baya ga ita kanta Holland tuni kasashen Jamus da Belgium da Sweden dama Switzerland suka fitar da miliyoyin kwayaye daga wuraren ajiyarsu don kare lafiyar al'ummarsu.

An dai yi zargin cewa gidajen gona a Holland sun cakuda sinadarin Fipronil da wani amintaccen maganin kwari don yiwa kaji da kwayaye fisa da nufin magance wasu cutuka.

Sinadarin Fipronil dai na daga cikin sinadaran da aka haramta yin amfani da su ga dabbobi musamman wadanda mutane ke ci la’akari da illar da zai iya haifarwa ga lafiyar bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.