Belgium

Fafaroma zai kori kungiyar 'yan Katolika

Fafaroma Francis kenan ke bayani kan rashin amincewarsu da bai wa marasa lafiya magani don a taimaka musu su mutu
Fafaroma Francis kenan ke bayani kan rashin amincewarsu da bai wa marasa lafiya magani don a taimaka musu su mutu REUTERS/Alessandro Bianchi

FAFAROMA Francis ya yi barazanar korar wata kungiyar agaji ta mabiya darikar katolika da ke kasar Belguim bayan gargadin da ya yi mata na dai na bai wa marasa lafiya maganin da ke taimaka musu wajen mutuwa ko kuma ya kore su.

Talla

Fafaroman ya ce suna mutunta rayukan jama’a saboda haka ba dai dai bane a dinga taimakawa marasa lafiya daukar ran su kawai saboda radadin ciwo.

Shugabannin gudanarwar kungiyar agaji ta Brothers of Charity a Belguim da ke da asibitoci 15 sun amince da bai wa marasa lafiya irin wannan taimako domin daukar ran su.

Tun a shekarar 2002 ne dai hukumomi a kasar ta Belguim suka halarta amfani da irin wannan magani don taimakawa marasa lafiyar da ke fuskantar tsananin radadin ciwo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.