Faransa

Yaki da safarar hodar ibilis a Faransa

Wata kotu a Faransa ta tisa keyar wasu mutane 14 da ake tuhuma da safarar hodar Ibilis daga tsibirin Dominican zuwa kotun dake yankin Bouches du Rhones a kudancin kasar.

hodar ibilis
hodar ibilis AFP/ Ernesto BENAVIDES
Talla

Ranar 19 ga watan Maris shekarar 2013 a filin tashi dama saukar jirage na Punta Cana dake kasar Dominican wani jirgin sama ya taso dauke da kusan kilogramme 700 na cocain zuwa Saint Tropez dake kudancin Faransa.

Wasu kungiyoyin masu zaman kan su a Faransa na ci gaba da yi kira zuwa hukumomin kasar da cewa ya dace hukuma ta mayar da hankali wajen sake gudanar da bicinke ,hakan na biyo bayan korafi da lauyoyin wasu faransawa biyu da ake tsare da su suka yi , Nicolas Pisapia da Alain Castany mutanen da kotu ta zartawa hukunci dauri na shekaru 20a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI