Faransa

Farin-jinin Macron na dada yin kasa a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Jean-Paul Pelissier

Soyayyar da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ke samu daga al'ummar kasar na disashewa a dai-dai lokacin da shugaban ke shirin cika kwananki 100 a karagar mulki.

Talla

Rahotan da Jaridar Le Figaro ta kasar ta wallafa ya bayyana yadda shugabanci Macron ke ci gaba da samun gagarumin koma baya a kwannaki 100 na shugabancinsa, wanda shi ne karon farko da ake samun haka tun bayan zamani Jacque Chirac a 1995.

Macron wanda ya dare karagar mulkin kasar a ranar 7 ga watan Mayun wannan shekarar kuma ya alkawaranta shawo kan rabuwar kawunan kasar, na fuskantar suka kan sabbin tsare-tsarensa na kwadago da rage kudadden kashewa, kasafi da kuma samar da ofishin matar shugaban kasa ga uwargidansa Brigitte mai shekaru 64.

Kazalika shugaban da ya kasance mafi karancin shekaru a tarihin mulkin kasar, na takun-saka da ma’aikatan gwamnati bayan ya kudiri aniyar dakatar da karin albashinsu.

A watan Yuni, jam’iyyar Macron ta Republican on the Move ta samu gagarumin rinjaye a Majalisa, wanda zai ba ta daman aiwatar da kudirorin shugaban.

Kamfanin Dilancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa, yanzu Macro yafi shugabannin Amurka da Rasha karfin fada aji ta fuskar diflomasiya a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.