Faransa

Farin jinin Macron na sauka cikin gaggawa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Reuters

Farin jinin shugaban Faransa Emmanuel Macron na ci gaba da raguwa a watanni ukun farko da fara mulkin kasar. Wani sabon rahoto da aka fitar yau Laraba ya nuna yadda kaso 37 cikin wadanda suka kadawa shugaban kuri’ar da ta kai shi ga mulkin kasar ne kadai ke farin cikin da kamun ludayinsa.

Talla

Farin jinin shugaba Emmanuel Macron mai shekari 39 dai raguwa cikin gaggawa tun bayan zabensa a watan Mayun daya gabata, a duk cikin binciken da aka dama sauraron ra’ayoyin jama’a kan farin jinin shugaban, binciken yau ya sha gaban kowanne inda ya tabbatar da yadda farin jinin shugaban ke kara dakushewa.

Wata tawagar masu binciken ta gudanar da gwaji kan mutane 994 inda kuma kaso 62 na adadin suka nuna rashin gamsuwarsu da kamun ludayin shugaban.

Macron mai matsakaicin ra’ayi dai ya yi nasara kan abokiyar takararsa mai tsattsauran ra’ayi Marine Le pen da kaso 66 na yawan kuri’a, lamarin daya kara girmama gadajjen rabuwar kan dake kasar.

Macron wanda da farko ya faro m,ulkin cikin bajinta, amma ana ganin saukar Donald Trump da Vladimir Putin na daga cikin abubuwan da suka jawo masa koma baya musamman ta fuskar yan adawa.

Haka kuma batun dokar kwadago dama ajje aikin babban hafson sojin kasar na daga cikin lamurran da suka yiwa shugaban lamba.

Ana kuma fargabar cewa shugaban ka iya fuskantar yajin aiki karon farko a kasar cikin watan Satumba sakamakon yunkurin dayake na sauya wasu dokokin kwadago.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.