Isa ga babban shafi
Portugal

Yan kwana-kwana na fafutukar ceto wasu mutane 2,000 a Macao

Jami’an kashe gobara a kauyen Macao na kasar Portugal
Jami’an kashe gobara a kauyen Macao na kasar Portugal REUTERS/Rafael Marchante
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Jami’an kashe gobara a kauyen Macao na kasar Portugal na fafutukar ceto wasu mutane 2,000 da wata gagarumar gobarar daji ta ritsa da su a tsakiya da kuma yankin arewacinsa.

Talla

Tuni dai gwamnati ta ayyana dokar ta baci a yankunan da gobarar dajin ta tashi, kamar yadda ministan cikin gidan kasar Costanca Urbano de Sousa ya tabbatar.

De Sousa ya zargi mutanen da ke zaune yankin da taimakawa wajen tashin gobarar, lamarin da ya kai ga cewa ba’a iya shiga ko fita daga kauyen na Macao saboda bakin hayyakin da ya turnuke, lamarin da ya haddasa gurbatar yanayin wajen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.