Faransa

Gobarar daji ta kawo tsaikon zirga zirga a Faransa

Tun bayan shigowar zafi wasu yankuna a nahiyar Turai ke fama da yawan tashin gobara
Tun bayan shigowar zafi wasu yankuna a nahiyar Turai ke fama da yawan tashin gobara Reuters

Sama da Fasinjoji dubu 3 a Kudancin Faransa suka makale a tasoshin jiragin kasa sakamakon mumunar gobarar dajin da ta mamaye hanyar jiragen da ya hada Birnin Marseille da Nice na kasar.

Talla

Akalla mutane 1,300 suka shiga rudani a Marseille, bayan dubu 1,700 da suka makale a Toulon wasu 370 kuma a birnin Nice bayan tashin gobarar a Aubagne, mai nisan kilimita 20 da gabashin Marseille, inda kuma ta bazu a kan hanyar da jiragen ke bi.

A cewar kamfanin jirgin kasa SNCF da ke Marsaille, jiragen kasa 10 ne suka samu tsaikon tsawon sa’o’I a makon da ya kasance mafi hada-hada jamaa a shekarar, saboda dawowa daga hutu, tsakanin Nice da Paris, wani lokaci kuma a ratsa ta Marseille.

Otel da dama da ke kusa da tashoshin sun cika makil, yayin da wasu kuma ala tilas suka kwana a cikin jirgin, kazalika SNCF ya yi kokari ciyar dasu abinci da abubuwan sha.

Mutane 3 da suka hada da masu kashe gobara da wata tsohuwa suka samu rauni a gobara, da ke kasance irinsa dake faruwa a ‘yan kwanankin nan a kudancin Turai tun shigowar zafi.

Kamfani dilanci Labaran Faransa, AFP ya rawaito cewa akasarin fasinjojin furgabansu shine karafuna hanyar jirgi da ya narke, sai dai a cewa SNCF babu wani gagarumin illa da shafar sufurin jiragen kasa da zata yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.