Holland

An fara gano masu hannu a yunkurin kai hari Holland

Jami'an 'yan sanda na ci gaba da sanya matakan tsaro a birnin Rotterdam na Holland bayan samun bayanai kan yunkurin kaddamar da harin ta'addanci.
Jami'an 'yan sanda na ci gaba da sanya matakan tsaro a birnin Rotterdam na Holland bayan samun bayanai kan yunkurin kaddamar da harin ta'addanci. Reuters

Jami’an yan sanda a Netherland sun fara tsananta bincike bayan samun wasu kwararan bayanai daga ‘yan sandan Spain da ke nuna cewa an shirya kaddamar da wani hari a Rotterdam yayin wani taron mawakan Amurka da aka shirya gudanarwa.

Talla

Babban jami’in ‘yan sandan birnin Frank Paauw ya shaidawa kamfanin dillancin labaran faransa na AFP cewa jami’an ‘yan-sandan Spain sun aike musu da wasu kwararan bayanan kan shirye-shiryen kaddamar da harin a casun da wasu mawakan Amurka za su gudanar a birnin Rotterdam na kasar.

Babu dai tabbacin ko samun bayanan na da alaka da kame mutane hudun nan da ke da hannu a harin Barcelona daya halaka mutum 15 baya ga jikkata 120.

Sai dai a yammacin jiya bayan dakatar da wani casu na ayarin mawaka Califonia, jami’an ‘yansandan sun kai sumame wani gida a kudancin Brabant tare da kame wani matashi mai shekaru 22 wanda suka ce yana da alaka da shirin kai harin na Rotterdam.

Haka zalika ko cikin daren jiya, ‘yansandan sun kama wani matukin babbar Mota bayan gano wasu tukunyar gas biyu a cikin motarsa, wanda kuma shima har yanzu ke rike a hannunsu duk da cewa bincike bai nuna yana da alaka da wata kungiyar ‘yan-ta’adda ba.

A cewar ministan shari’ar kasar Stefan Blok za a ci gaba da tuhumar matashin don gano gaskiyar dalilan da suka sanya shi yunkurin kai farmaki a kasar.

Ko a watan mayun daya gabata ma dai kimanin mutum 22 ne suka mutu a wani hari da aka kaddamar yayin wani casu da mawakiyar Amurka Ariana Grande ta gudanar a Manshester.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.