Isa ga babban shafi
Faransa

Turai: Macron na jagorantar taron magance kwararar bakin haure

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Reuters/Stoyan Nenov
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
2 min

A wannan Litinin Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ke jagorantar jagoranci taron kasa da kasa kan yadda za a tunkari matsalar kwararar baki zuwa Turai.

Talla

Taron da ke gudana a birnin Paris, zai samu halartar shugabannin wasu kasashen yankin Turai, daga ciki akwai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da takwaran aikinta na Italiya Paolo Gentiloni da kuma na Spain Mariano Rajoy, yayin da daga nahiyar Afirka Afirka za a samu halartar shugaban Nijar Issifou Mahamadou, da na Chadi Idris Deuy, sai kuma shugaban gwamnatin hadin-kan kasar Libya Fayez al-Sarraj.

Babban abin da taron zai mayar da hankali a kai shi ne duba yadda za a magance matsalar baki daga kasashen Afirka, Yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Asiya wadanda ke kwarara zuwa Turai, yankin da ke samun wakilcin Frederica Moghreni a wannan taro.

Sanarwar da fadar shugaban Faransa ta fitar, ta ce an gayyaci shugabannin kasashen Nijar, Chadi da kuma Libya zuwa wannan taro ne lura da cewa za su iya taka gagarumar rawa wajen magance wannan matsala ta kwararar baki.

A ranar 9 ga wannan wata na Agusta, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, ya ce kasar tana shirin kafa wasu cibiyoyi na musamman a cikin Libya, domin tantance bakin da suka cancanci samun izinin wucewa zuwa nahiyar Turai, domin fara aiwatar da shirin rage yawan wadanda ke amfani da kananan jiragen ruwa domin tsallaka tekun Mediterranean.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.