Isa ga babban shafi
Girka-Faransa

Emmanuel Macron ya shiga rana ta biyu a ziyar da ya kai Girka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na jawabi a birnin Athens na Girka
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na jawabi a birnin Athens na Girka Reuters
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim | Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci asusun bayar da lamuni na duniya, IMF da ya nuna kyakkyawar aniya  dangane da kokarin ceto Girka daga  matsalar bashin da kasar ke fama da ita.

Talla

Shugaba Macron ya fadi hake a birnin Athens a yayin da da ya ke gudanar da ziyarar kwanaki biyu a Girka, kuma a dai dai lokacin da ya rage watanni 11, wa’adin ceto  Girka ya cika.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa, muddin asusun na son taka rawa a shirin ceto Girka daga kangin bashi, to  ya dace ya nuna kyakkyawar aniya  ba tare da kara gindaya wa kasar wasu sharudda ba.

Karo na uku kenan da ake samar da tsare-tsaren fitar da Girka daga matsalar  bashin, kuma a halin yanzu, kungiyar Turai ce ke daukar dawaniyar ceto kasar nan da watan Agustan 2018.

IMF ya ce, ba zai sanya kobo ba a shirin ceto Girka daga bashin har sai wadanda ke bai wa  kungiyar tarayyar Turai rance sun dada sassauta wa Girkan dimbin bashin, abin da har yanzu ake kai ruwa rana musamman ganin yadda Jamus ke ci gaba da nuna tirjiya.

Shugaba Macron ya nuna damuwa da matakin da kungiyar ta EU ta dauka na neman agaji daga waje kafin  samun nasarar ceto Girka a shekarar 2010, abin da ya fito da rashin jituwa  tsakanin  kasashen yankin da  wasu manyan cibiyoyi.

 

  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.