Bakonmu a Yau

Dr Abba Sadiq kan sabuwar dokar yaki da ayyukan ta'addanci a Faransa

Sauti 03:18
Amincewa da dokar yaki da ayyukan ta'addancin a Faransa na zuwa ne a daidai lokacin ake samun yawaitar ayyuka masu alaka da hakan.
Amincewa da dokar yaki da ayyukan ta'addancin a Faransa na zuwa ne a daidai lokacin ake samun yawaitar ayyuka masu alaka da hakan. Reuters

A jiya talata ne Majalisar Dokokin Faransa ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar dokar yaki da ayyukan ta’addanci a kasar, lamarin da yai kawo karshen aiki da dokar ta bacin da aka kafa tsawon shekaru biyu da suka gabata a kasar. A karkashin wannan doka, an bai wa jami’an tsaron kasar karfin ikon cafke duk wanda ake zargi da ayyukan ta’addanci ko kuma yunkurin kawo cikas ga tsaron kasar. A zantarwarsu da Abdooulkarim Ibrahim Shikal, Abba Sadiq, wani dan jarida ne da ke zaune a birnin Paris, ya bayyana mana wasu daga cikin abubuwan da dokar ta kunsa.