spain

Firaministan Spain ya gargadi shugabancin Catalonia

Firaministan Spain Mariano Rajoy ke jawabi yayin wani taro kan rikicin siyasar kasar.
Firaministan Spain Mariano Rajoy ke jawabi yayin wani taro kan rikicin siyasar kasar. Reuters

Firaminstan Spain Mariano Rajoy ya yi gargadin cewa, gwamnatin kasar za ta iya amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta wajen dakatar da shugabancin yankin Catalonia matukar ya ci gaba da bukatar neman ‘yancin kai.A baya bayan nan dai Al'ummar Catalonia sun tsananta gudanar da gangami don tabbatar da 'yancin yankin nasu a Gobe Litinin.

Talla

Gargadin Firaministan na zuwa ne kwana guda bayan an gudanar da wasu mabanbantan gangami a sassan kasar biyu, inda masu gangami a Madrid ke bukatar hadin kan kasar, yayinda wadanda suka gudanar da nasu a Barcelona kuma suka bukaci tattauna da gwamnatin kasar don bai wa yankin ‘yancin kai.

Rajoy ya kuma yi watsi da bukatar tattaunawa da shugabancin yankin na Catalonia dangane da batun ‘yancin, baya da suka kada kuri’ar raba gardamar ballewa daga Spain ranar 1 ga watan nan wadda ya ce ta sabawa tanadin kundin tsarin mulkin kasar na 1978.

Tun kafin yanzu dai gwamnatin ta Spain ta sha ayyana kuri'ar raba gardamar ballewar yankin na Catalonia a matsayin haramtacciya wadda ta ce ta saba da tanadin dokokin kasar.

Haka zalika yayin da al'ummar ta Catalonia suka yi fitar dango don kada kuri'ar a ranar 1 ga watan Oktoba, gwamnatin ta yi amfani da karfin jami'an tsaro wajen tarwatsasu, yayinda 'yansanda suka yi amfani da harsashin roba wanda ya jikkata mutane da dama.

A makon da ya gabata ne dai Gwamnatin ta fitar da sanarwar neman yafiya kan abin da ya faru inda a bangare guda kuma ta kara gargadin 'yan Cataloniyar kan kada su kara yunkurin haka.

Duk da haka dai har yanzu al'ummar yankin na Catalonia na ci gaba da fafutukar ganin sun balle daga Spain yayin da su ke jiran jawabin jagoransu Carles Puidgement a gobe Litinin don ya ayyana yankin a matsayin mai cin gashin kan sa.

Al'ummar Catalonia dai na da yawan akalla mutum Milyan 7 da rabi kuma yare da al'adunsu daban ne dana mutanen Spain.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.