Spain

Shugaban Catalonia na fuskantar matsin lamba

Shugaban yankin Carles Puigdemont na gabatar da jawabi a taron manema labarai a birnin Barcelona
Shugaban yankin Carles Puigdemont na gabatar da jawabi a taron manema labarai a birnin Barcelona LLUIS GENE / AFP

Shugaban yankin Catalonia da ke neman ballewa daga kasar Spain, Carles Puigdemont na ci gaba da fuskantar matsin lamba don ganin ya janye shirinsa na sanar da ballewar yankin a jawabin da zai yi wa Majalisa a yau.

Talla

Mai rike da mukamin Magajin Garin Barcelona, Ada Colau ta bukaci Puigdemont da Firaministan Spain Mariano Rajoy da su kawo karshen wannan tankiyar ta hanyar tattaunawa.

Tuni kasashen Faransa da Jamus suka bayyana rashin amincewarsu da matakin da kuma goyan bayan Spain a matsayin kasa guda.

Ministar kula da sha’anin Turai, Natalie Loiseau ta ce, idan har yankin Catalonia ya sanar da cin gashin kai to Faransa da Tarayar Turai ba za su goyi bayan matakin ba.

Yankin na Catalonia dai na da matukar tasiri ga tattalin arzikin Spain, yayin da  rahotanni ke cewa, kamfanoni da dama sun fara ficewa saboda adawa da ballewar yankin daga Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.