Amurka

Amurka zata bayyana kundin sirri kan kisan gillar John F. Kennedy

Shugaban Amurka John F. Kennedy, ta re da mai dakinsa Jaqueline Kennedy, tafe tare da gwamnan jihar Texas, John Connally mintuna kadan kafin a yi masa kisan gilla a Dallas, dake jihar Texas,  22 ga watan Nuwamba, 1963.
Shugaban Amurka John F. Kennedy, ta re da mai dakinsa Jaqueline Kennedy, tafe tare da gwamnan jihar Texas, John Connally mintuna kadan kafin a yi masa kisan gilla a Dallas, dake jihar Texas, 22 ga watan Nuwamba, 1963. REUTERS

Bayan shekaru Hamsin da kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban Amurka John F. Kennedy, gwamnatin Shugaba Donald Trump na daf da fitar da wasu kundayen bayanan sirri fiye da 3000 da suka kunshi sakamakon binciken da aka gudanar kan kisan.

Talla

Sau da dama ana gudanar da bincike kan kisan, sai dai ba’a taba fitar da kundayen bayanan sirrin ba, kamar wanda za’a yi a yau.

A bayanan da shugaba Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce za’a fitar da takardun ne fiye da dubu 3 don cigaba da bincike kan kisan gillar Shugaba John F Kennedy, a wani mataki na sabunta yunkurin gano wadanda suka hada hannu don aiwatar da kisan gillar.

Har yanzu dai akwai shakku kan ko makashin Kennedy Lee Harvey Oswald ya hada hannu da wasu wajen kisan ko a’a.

A watan Nuwamban shekara ta 1963, aka yi wa John F. Kennedy kisan gilla, bayan shafe shekaru biyu yana shugabantar Amurka.

Kafin wannan lokacin hukumomin tsaron Amurka sun kauracewa fitar da bayanai kan kisan, matakin da suka ce sun dauki shi ne bisa dalilai na tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.