Catalonia

Zan ci gaba da zama a Brussels - Puigdemont

Carles Puigdemont ya kira taron manema labarai domin bayyana matsayarsa a Brussels
Carles Puigdemont ya kira taron manema labarai domin bayyana matsayarsa a Brussels REUTERS/Yves Herman

Shugaban yankin Catalonia wanda aka tube Carles Puidgemont da yanzu haka ke zaune a kasar Belgium, ya ce zai cigaba da zama a birnin Brussels saboda dalilai na tsaro.

Talla

Puigdemont wanda ya kira taron manema labarai ranar Talata a Brussels ya ce zaman sa a Belgium ba yana nufin cewa ya je ne domin neman mafaka a kasar ba.

Tun bayan tumbuke gwamnatinsa a ranar Juma’ar da ta gabata, Puigdemont tare da kusoshin gwamnatinsa a jiya Litinin suka bar yankin zuwa birnin Marseille da ke kudancin Faransa, kafin daga bisani kuma ya tsallaka Belgium.

A cewar Puigdemont wanda bai sanar da ranar da zai koma Spain ba, shi da mukarrabansa za su cigaba da zama a Brussels saboda samun cikakken ‘yanci da kuma al’amuran da suka shafi tsaro.

A jawabin da ya gabatar ga taron manema labarai, tubabben shugaban ya ce za su zuba ido a kan zaben da Firaminista Mariano Rajoy ke shirin gudanarwa ranar 21 ga watan Disamban 2017.

Da safiyar ranar Talata ne kotun tsarin mulkin Spain ta sanar da haramcin ayyanawar da Puigdemont ya yi wa yankin na Catalonia a matsayin kasa cikin makon da ya gabata.

A bangare guda kuma kotun kolin kasar ta yi sammacin kakakin majalisar dokokin Catalonia Carme Forcadell da ta bayyana gabanta ranar 2 da 3 ga watan Nuwamba mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI