Spain-Calatonia

Kotun Spain ta tsare mambobin gwamnatin Puigdemont

Wasu daga cikin Mambobin gwamnatin Puigdemont da aka tsare a Spain
Wasu daga cikin Mambobin gwamnatin Puigdemont da aka tsare a Spain GABRIEL BOUYS / AFP

Kotun Spain ta bada umarni tsare tsoffin mambobin gwamnatin Catalonia da aka tube, ciki hada mataimakin shugaban yankin, bayan Carles Puidgemont ya kauracewa zaman kotun.

Talla

Kotun da ke zamanta a Madrid ta ba da wannan umarni ne bayan ritsa mambobin da tambayoyi kan rawar da suka taka wajen bukatar balewar Catalonia, ko da dai tubeben Shugaban Yankin Carles Puigdemont da ke zaune yanzu haka a Belgium ya kauracewa kotun.

Puigdemont da mukarrabansa 19 sun samu sammacin alkalan kotunan Spain da suka hada da Kotun kasa da kuma kotun koli a ranakun Alhamis da Juma’a, kan zargin ingiza rikici, tawaye da almubazaranci da kudadden gwamnati.

Sai dai an dage sauraron karar kotun kolin zuwa 9 ga watan Nuwamba, sakamakon alfarmar da lauyoyi suka nema na basu karin lokacin kimtsa kare kansu, yayin da ake ci gaba da sauraron karar da aka shigar a gaban Babban Kotun kasar.

A yanzu dai Kotun ta bada daman tsare 8 daga cikin tsoffin mabobin gwamnatin Puidgemont da suka halara a gabanta kamar yadda masu gabatar da kara suka bukata.

Bayan Puigdemont, akwai kuma tsoffin ministoci 4 da suma suka ki halara a gaban kotun, lamarin da ya sa masu gabatar da kara neman a ba da sammacin cafkesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.