Shekaru biyu da kai harin Bataclan a Paris
Wallafawa ranar:
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tareda rakiyar tsohon Shugaban kasar Francois Hollande sun halarci gangamin yi tuni da mutanen da suka rasa rayukan su a harin ranar 13 ga watan Nuwemba shekarar 2015 a birinin Paris, hari na Bataclan inda mutane 130 suka rasa rayukansu.
Shugaban kasar Emmanuel Macron ya bayyana alhinin sa tareda jaddada cewa Faransa zata yaki ta'addanci, indan aka yi tuni Hukumomin Faransa a lokacin harin sun bayyana wani matashi a matsayin mutun na uku da ke da hannu a hare haren ta’addancin da kungiyar ISIS ta kai a birnin Paris, inda mutane 130 suka rasa rayukansu.
Foued Mohamed Aggad mai shekaru 23 na da hannu a harin da aka kai a gidan rawa na Bataclan.
Aggad ya tafi kasar Syria tare da dan uwansa da wasu na kusa da shi a karshen shekara ta 2013, kuma jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu daga cikin su bayan sun dawo Faransa .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu