Turkiya

EU za ta zaftare tallafin da ta ke bai wa Turkiya

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan. REUTERS/Umit Bektas

Kungiyar tarayyar turai Eu ta ce zata zaftare kudaden da take bai wa kasar Turkiya a matsayin taimako, sakamakon yadda gwamnatin Recep Tayyib Erdogan, ke kokarin karya tsarin Dinkoradiyya.

Talla

Kungiyar ta ce zata zaftare yawan kudaden da suka kai euro miliyan 105, sai kuma karin euro miliyan 70, da zata zaftare daga kasafin shekara ta 2018 da ta warewa kasar ta Turkiya.

Euro bilyan 4.5 ne ya kamata EU ta bai wa Turkiya, a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2020, a matsayin tallafi ga kasar, domin cimma ka’idojin da kungiyar ta gindaya mata, kafin bata damar shiga cikinta.

A halin yanzu kasashen na EU na dakon amincewar majalisar zartawa da kuma majalisar wakilan kungiyar, kafin fara aiwatar da kudurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.