Faransa

Faransa ta buƙaci Isra'ila ta daina gine-gine a yankin Falasɗinawa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya buƙaci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya daina gine-gine a yankunan Falasɗinawa da kuma ƙaddamar da tattaunawa domin kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Isra'ila Natenyahu lokacin taron manema labarun, December 10 2017.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Isra'ila Natenyahu lokacin taron manema labarun, December 10 2017. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Yayin da yake jawabi bayan ganawar da suka yi a birnin Paris, shugaba Macron ya ce daina gine-gine zai bai wa Falasɗinawan ƙwarin gwuiwar tattaunawa da gwamnati.

Shugaba Macron na daga cikin na gaba-gaba wajen bayyana adawa da shirin Amurka na tabbatar da birnin Ƙudus a matsayin babban birnin Israila da kuma kiran taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cikin gaggawa wanda ya yi Allah-wadai da matakin.

Yanzu haka Netanyahu na ziyara a Turai, inda zai gana da ministocin harkokin waje na ƙasashen yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI