Amurka

Gobarar dajin California ta zama mafi muni a tarihin jihar

Gobarar dajin "Thomas" da ta tayi mummunar barna a jihar California, Amurka. Disamba 9, 2017.
Gobarar dajin "Thomas" da ta tayi mummunar barna a jihar California, Amurka. Disamba 9, 2017. REUTERS/Gene Blevins

Gobarar dajin da ta lalata sama da gidaje 700 a Carlifornia, ta zama mafi muni da ta taba aukuwa a jihar.

Talla

Gobarar wadda aka yi wa lakabi da Thomas, ta kone fadin kasa da ya zarta murabba'in kilomita dubu 1,000, girma da fadin da ya zarta na biranen New York, Brussels da kuma Paris idan aka gama su waje guda.

Gobarar dajin ta tashi ne a Santa Paula cikin farkon watan Disamba da muke ciki, inda aka aike da jami’an kashe gobara sama da dubu 8000, domin shawo kanta.

Masana kimiyya sun danganta yawaitar tashin gobarar dajin da dumamar yanayi, da kuma kusantar dazuka da gidajen al’umma ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.