Isa ga babban shafi
Faransa

Kankara ta haddasa cinkoso a Paris

Kankara ta mamaye sassan birnin Paris na Faransa
Kankara ta mamaye sassan birnin Paris na Faransa REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Dusar kankara ta haddasa cinkoson ababan hawa tare da tilas dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a birnin Paris na Faransa.Mahukuntan kasar sun bayyana zubar dusar a matsayin mafi muni a wannan kakar ta bana.

Talla

Hukumar kula da yanayi ta Faransa ta sanya birnin Paris cikin shirin ko-ta-kwana saboda tsananin zubar kankara da ta cinkushe manyan hanyoyi a birnin Paris.

Matsalar ta haifar da cinkoson ababan hawa a sassan birnin, in da cinkoson ya mamaye tsawon tafiyar sama da kilomita 700, kuma ana ganin watakila matsalar ta yi kamari a cikin wannan makon.

Direbobin motoci sun yi ta bayyana bacin ransu bayan shafe tsawon sa’oi a cikin tsananin sanyi kuma a cikin dogayen layukan ababan hawa a kan tituna.

Tuni wasu kamfanonin motocin haya suka jingine ayyukansu, kamar yadda wasu makarantun boko suka dakatar da zirga-zirgar motocinsu.

Suma dai jiragen kasa ala dole suka rage gudunsu don kauce wa gamuwa da hatsari saboda kankarar da ta mamaye layin dogo, yayin da a bangare guda aka rufe hatsumiyar Effel da ke birnin na Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.