Isa ga babban shafi
Amurka

Tsohon dalibi ya hallaka 'yan makaranta 17

Wasu daga cikin daliban makarantar 'Marjory Stoneman Douglas High School' a Florida da ke Amurka, yayin da ake kwashe su, bayan harin da wani tsohon dalibi ya kai inda ya hallaka dalibai 17.
Wasu daga cikin daliban makarantar 'Marjory Stoneman Douglas High School' a Florida da ke Amurka, yayin da ake kwashe su, bayan harin da wani tsohon dalibi ya kai inda ya hallaka dalibai 17. Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Wani tsohon dalibin wata makaranta dake Florida a kasar Amurka, ya bude wuta kan daliban makarantar inda ya kashe 17 daga ciki.

Talla

Scott Israel, jami’in tsaro a Yankin Broward County, ya bayyana dalibin a matsayin Nikolas Cruz, wanda aka kora daga makarantar saboda aikata wasu laifuka.

Tuni jami’an tsaro suka kama Cruz, wanda yanzu yake amsa tambayoyi.

Gwamnan Florida, Rick Scott, ya bayyana kisan ta’addancin a matsayin mugunta karara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.