Isa ga babban shafi
France-Liberia

Shugaban Liberia George Weah Na Ziyara A Faransa

Shugaba George Weah tare da matarsa cikin wani hoto da aka dauka a  Monrovia ranar  22 ga watan Janairu 2018
Shugaba George Weah tare da matarsa cikin wani hoto da aka dauka a Monrovia ranar 22 ga watan Janairu 2018 rfi
Zubin rubutu: Garba Aliyu
1 min

Sabon shugaban kasar Liberia George Weah ya yi alkawarin tsabtace kasar sa daga matsalar cin hanci da rashawa, inda yake cewa bai gaji komi ba cikin asusun Gwamnatin.

Talla

George Weah na Magana ne a Paris na kasar Faransa a ziyarar farko da ya kai wata kasa tun bayan rantsar dashi a ranar 22 ga watan Janairu.

Tsohon dan wasan kwallon kafan na duniya ya yi alkawarin ganin anyi kididdigan dukiya da kaddarorin Gwamnati.

Ya sanar da cewa ya bukaci ayi babban garambawul ta fannin ilmi  saboda muhimmancin ilmi ga biladama.

Laraba ne kuma George Weah zai gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.