Spain-Calatonia

Za a sake kada kuri'ar ballewar Catalonia daga Spain

Manyan jam’iyyun ‘yan awaren yankin Catalonia sun bukaci sake kada kuri’ar raba gardamar ballewar yankin daga kasar Spain don zamowa kasa mai cin gashin kanta. 

Catalonia na muradin ballewa daga Spain don cin gashin kansa
Catalonia na muradin ballewa daga Spain don cin gashin kansa REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Cikin wata yarjejeniya da manyan jam’iyyun suka cimma a yau akwai batun kafa wata gwamnati ta daban sabanin ta yankin na Catalonia wanda yanzu ke ci gaba da kasancewa karkashin ikon Spain.

Jam’iyyun sun cimma matsayar nada tubabben shugaban yankin da ke gudun hijira a Belgium, Carles Puidgemont a matsayin wanda zai shugabanci sabuwar gwamnatin da za su kafa.

Kazalika daga cikin yarjejeniyoyin da jam’iyyun suka cimma, akwai kuma batun fasalta kundin tsarin mulkin yankin da zai kai ga kafa sabbin sassan gwamnati masu cikakken iko ba tare da hadaka da gwamnatin yankin ta yanzu ko kuma gwamnatin Spain baki daya.

Tun a ranar 27 ga watan Oktoban bara ne yankin na Catalonia karkashin jagorancin shugabansa, Carles Puidgemont ya kada kuri’ar ‘yancin yankin tare da ayyana kansa a matsayin ‘yantacce, matakin da ya tilasta wa gwamnatin Spain tsige shugabancin yakin tare da kafa sabuwar gwamnati, baya ga daure wasu daga cikin shugabannin yankin, yayin da wasu kuma suka yi gudun hijira.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI