Faransa

Ina son National Front ta koma National Rally- Le Pen

Marine Le Pen ta jam'iyyar National Front a Faransa
Marine Le Pen ta jam'iyyar National Front a Faransa REUTERS/Pascal Rossignol

Shugabar Jam’iyyar National Front ta masu tsattsauran ra’ayi a Farasa, Marine Le Pen ta bukaci sauya sunan jam'iyyar zuwa National Rally, a wani yunkuri na dawo da martabar jam'iyyar wadda jama'a ke alakanta ta da nuna wariyar launin fata.

Talla

Kazalika matakin sauya sunan zai sauwake wa jam’iyyar hada kai da wasu jam’iyyun siyasa a kasar.

A lokacin da ta ke jawabi a taron da jam’iyyar ta gudanar a karshen mako, uwargida Le Pen da ta sha kashi a hannun shugaba Emmanuel Macron a cikin watan Mayun bara, ta ce, babbar manufar jam’iyyra ita ce, karbe mulki ta hanyar hada kai da wasu jam’iyyu don cimma wannan muradi.

Dimbin magoya bayan jam’iyyar rike da alluna sun yi ta kambama Le Pen a yayin jawabinta, in da kuma suka yi tir da tsarin shige da fice na kasar da kuma dunkulewar kasashen Turai.

Le Pen ta ce, duk da cewa, jam’iyyarsu ta samo asali ne daga zanga-zanga, amma babu shakka za ta iya zamowa jam’iyya mai mulki a Faransa.

Sai dai kawo yanzu kashi 52 cikin 100 na mambobin jam’iyyar ne suka goyi bayan sauya sunan kamar yadda wasu alkaluma da jam’iiayyar ta fitar suka nuna a ranar Asabar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI