Saudiya-Syria

Bukatar Saudi Arabia na aikewa da dakaru zuwa Syria

Taswirar kasashen Daular Larabawa
Taswirar kasashen Daular Larabawa

Hukumomin Kasar Saudi Arabia sun bukaci Amurka ta basu damar girke sojojin su a kasar Syria domin aiki da kawancen da sojojin ta ke jagoranci.

Talla

Ministan harkokin wajen Saudiya, Adel al-Jubeir yace suna tattaunawa da jami’an gwamnatin Amurka tun barkewar yakin Syria a shekarar 2011 kan bukatar ta su na tura sojojin kasashen su.

Ministan yace tun lokacin gwamnatin Barack Obama suka bayyana aniyar su na bada sojojin muddin Amurka ta amince ta tura sojoji cikin kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.