Belgium-Syria

An zargi wasu kamfanoni kasar Beljiyom 3 da shigar da sinadaran mai guba a Syriya

Isopropyl sanadarin harhada magungunan da makamai masu guba
Isopropyl sanadarin harhada magungunan da makamai masu guba westchem.com

Ana zargin wasu kamfanonin kasar Belgium da shigar da sinadirrai da ake iya yin amfani da su domin sarrafa makami mai guba a kasar Syria, kuma a cewar wata majiya a ma’aikatar shara’ar kasar, za a gurfanar da shugabannin kamfanonin da ake zargin gaban kotu a ranar 15 ga watan mayun gobe.

Talla

Kamfanoni 3 ne, ake zargi da fataucin sinadirin Isopro-panol wanda ake iya amfani da shi domin kera makamai masu guba ko samar da sinadirin sarin zuwa kasar ta Syria tsakanin 2014-2016 duk da cewa kafin lokacin an riga an sanya takunkumin da ke hana shigar da irin wannan sinadiri a kasar ta Syria.

Isopropanol, sinadiri ne da ya kamata a yi amfani da shi domin sarrafa magunguna, fenti da kuma sauran sinadiran tsaftace muhalli, to sai dai za a iya amfani da shi domin hada iskar gaz mai guba da ke kisa nan take.

Ma’aikatar hana fasa kori ta kasar Belgium wadda ta kaddamar da bincike kan wannan zargi, ta ce akalla ton 96 na wannan sinadiri ne kamfanonin suka shigar a Syria, yayin da wasu bayanai ke cewa an shigar da su ne lokuta daban daban har sau 24 domin kauce wa sa-idon kasashen duniya.

Kamfanonin da ake zargin sun bayyana cewa dukkanin hajojin da suka shigar a Syria, sun shigar da su ne da amincewar hukumar hana fasa kori ta kasar.

A ranar 15 ga watan mayu mai zuwa ne shugabannin kamfanonin uku za su gurfana gaban kotu a birnin Anvers domin fara shara’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.