Belgium-France

Kotun Belgium ta samu Abdesalam da laifin ta'addanci

Kotun Belgium ta samu Salah Abdeslam, mutun na karshe da ake zargi da hannu a kazamin harin da kungiyar ISIS ta kai birnin Paris, da laifin ayyukan ta'adanci bayan ya yi kokarin kisa a wata  musayar wuta da jami’an ‘yan sanda a birnin Brussels kwanaki kalilan kafin cafke shi a shekarar 2016. Ana saran nan gaba kadan kotun ta yanke masa hukunci.

Salah Abdesalam da ake zargi da hannu a harin birnin Paris da kuma musayar wuta da 'yan sanda a birnin Brussels
Salah Abdesalam da ake zargi da hannu a harin birnin Paris da kuma musayar wuta da 'yan sanda a birnin Brussels REUTERS
Talla

A cikin watan Fabairun da ya gabata ne aka bukaci masu shigar da kara da su daure Abdesalam shekaru 20 a gidan yari matukar aka same shi da laifin da ke da alaka da ayyukan ta’addanci da kuma mallakara haramtattun makamai.

Abdesalam,wanda ke tsare a gidan yarin Faransa gabanin yanke masa wani hukuncin daban kan harin 2015 a birnin Paris da ya kashe mutane 130, bai samu  halartar zaman shari'ar na yau ba a Brussels tare da Sofine Ayari da ake zargin su tare da aikata laifin.

Mai gabatar da shari'a a kotun, Marie-France Keutgen ta shaida wa kotun cewa, Abdesalam da Ayari ba za su samu damar halartar zaman ba a yau.

Za a shafe kiman sa’oi uku ana bitar laifin da ake zargin su da aikatawa kafin yanke hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI