Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya cika shekara daya bisa shugabancin Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Vincent Kessler
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

A kwana a tashi, yau 7 ga watan Mayu, shekara daya kenan tun bayanda aka zabi Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasar Faransa.

Talla

Macron dai ya yi nasara a zaben ne sakamakon gabatar wa da ‘yan kasar wasu manufofi irin na masu tsaka-tsakin ra’ayi.

Shugaban na Faransa, ya kafa tarihin zama na farko mafi kankantar shekaru ne bayan da yayi ya doke abokiyar hamayyarsa ta jam’iyyar masu zazzafan ra’ayi Marine Le Pen da akalla kashi 66 cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben shugabancin kasar.

Duk da cewa ra’ayoyin jama’ar Faransa sun sha bambam a game da kamun ludayin matashin shugaban kasar, a matakin kasa da kasa ana kallon Macron a matsayin wanda ke da kyakkyawar siyasar samar da sauyi musamman a yankin Turai.

Baya ga ziyarce-ziyarce zuwa manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka, China, India da kuma Australia, hakazalika Emmanuel Macron ya karbi bakuncin fitattun mutane a fadarsa da ke Paris, da suka hada da Vladimir Putin na Rasha, Abdel Fatah al-Sisi na Masar da kuma Yerima Mohammed bin Salman mai jiran gadon sarautar Saudiyya.

A watannin farko bayan darewarsa kan karagar mulki, Macron ya ziyarci wasu kasashe na Afirka, to sai dai a cikin gidan Faransa yana fuskantar manyan kalubale sakamakon sauye-sauyen da yake kan aiwatarwa a fannonin da suka hada da dokar yaki da ayyukan ta’addanci, makomar baki da kuma ayyukan kwadago.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.