Cataloniya

Carles Puigdemont, ya yi watsi da sake nada shi Shugaban Catalonia

Carles Puigdemont, ya yi watsi da Shugabancin Catalonia daga Berlin
Carles Puigdemont, ya yi watsi da Shugabancin Catalonia daga Berlin Handout / YOUTUBE / AFP

Carles Puigdemont, tubabben shugaban yankin Catalonia da ke gudun hijira a Jamus, ya yi watsi da sake nada shi da aka yi matsayin shugaban yankin mai neman ballewa daga Spain.

Talla

Puigdemont ya bayyana a wani sakon ta faifan bidiyo cewa ba ya bukatar wannan mukami, bayan da majalisar dokokin yankin na Catalonia ta kada kuri’ar da ke ba shi wannan dama duk da cewa ba ya zaune a cikin kasar..

A baya jawaban da Puigdemont ya gabatar yayin gangamin daya gudana a Belgium, ya ce lokaci yayi da ‘yan Catalonia za su kara nuna jajircewarsu kan bukatar da su ke da ita na kasancewa yankin kasa mai cin gashin kan shi.

Puigdemont wanda ke tsare a Berlin tun bayan kwace kwarya-kwaryan ikon da Spain ta yiwa yankin na Catalonia a ranar 27 ga watan Oktoba shekarar 2017, yanzu haka Spain na zarginsa da cin amanar kasa, amfani da kudade a wurin da basu dace ba, baya ga amfani da kujerarsa wajen tunzura al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.