Isa ga babban shafi
Turai

Tarayyar Turai na tattauna yadda za ta mayarwa Trump martini

Jakadiyar harkokin wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini.
Jakadiyar harkokin wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini. Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman | Azima Bashir Aminu
Minti 2

Shugabannin kasashen tarayyar Turai, na taro a Bulgaria, don cimma matsaya kan martanin da za su maidawa Amurka, dangane da janyewarta daga yarjejeniyar Iran, da kuma kakaba sabon haraji akan wani sashi na kasuwancin da ke tsakaninsu.

Talla

Kafin matakan na baya bayan nan da Trump ya dauka dai da farko taron shugabannin kasashen turan zai tattauna ne kan alakarsu da kasashen yankin Balkan da ke kudu maso gabashin nahiyar Turai.

Sai dai a yanzu lamarin ya sauya inda a yau wakilan kasashen Turan 28 ke tattaunawa kan raddin da ya kamata su mayarwa Amurka dangane da sabbin takunkuman da ta kakabawa Iran bisa zarginta da yunkurin mallakar makaman Nukiliya, wadanda Amurkan ta ce za su shafi dukkanin kamfanoni ko kasashen da suka ki yanke hulda da kasar ta Iran.

Sauran manyan batutuwan da suka mamaye taron akwai sabon tsarin harajin da Donald Trump ya kakkaba kan kayayyakin Karafa da Alminium da ake shigar da su Amurka, sai kuma batun kisan Falasdinawa fiye da 60 baya ga jikkata kusan 300 da Isra'ila ta yi boren da suka yi kan adawa da matakin Amurkan na mayar da ofishin jakadancinta zuwa birnin Kudus, matakin da shi ma tarayyar Turan ke adawa da shi.

A yanzu ana dakon, shugabar sashin lura da harkokin waje na trayyar turai Federica Mogherini da kuma shugaban hukumar kungiyar Jean-Claude Juncker su bayyana yadda za su kare manufofi da kamfanoninsu daga takunkuman Amurkan kan Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.