Isa ga babban shafi

Al'ummar Venezuela na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro. Juan BARRETO / AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Al’ummar Venezuela suna kada kuri’a a zaben shugaban kasar a yau Lahadi, zaben da ‘yan adawa suka kauracewa bisa zargin za a tafka magudi.

Talla

Bayan fara wa’adin shugaba mai ci Nicolas Maduro daga shekarar 2013 zuwa yanzu, Venezuela ta tsinci kanta cikin koma bayan tattalin arziki da yayi sanadin karancin abinci da magunguna da kuma karuwar aikata laifuka, dalilan da suka haifar da zazzafar zanga-zangar adawa da gwamnati tsawon watanni.

Sai dai duk da haka ana sa ran Nicolas maduro ne zai yi nasara a zaben, la’akari da cewa manyan jami’yyun adawar kasar sun ki marawa abokin hamayyarsa baya Henri Falcon, wanda tsohon sojan kasar ne.

A ranar Asabar da ta gabata shugaba Maduro ya zargi Amurka da amfani da takunkuman karya tattalin arziki da ta kakaba mata wajen yiwa shirin zaben shugabancin kasar zagon kasa.

A ranar Juma’ar da ta wuce, a karon farko Amurka ta alakanta shugaban na Venezuela da safarar miyagun kwayoyi, abinda ya sa ta daukar matakin karawa gwamnatin kasar wasu takunkuman na dabam da wadanda ke aiki akanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.