Isa ga babban shafi
Faransa

Netanyahu zai gana da Macron na Faransa a yau

Fira Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a birnin Berlin na Jamus
Fira Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a birnin Berlin na Jamus REUTERS/Axel Schmidt
Zubin rubutu: Faruk Yabo
2 Minti

Yau talata Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu zai gana da shugaba Emmanuel Macron na Faransa a birnin Paris, a ci gaba da ziyarar wasu kasashen Turai domin ganin cewa sun yi koyi da Amurka wajen yin watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Talla

A lokacin da yake ganawa jiya litinin da waziyar Jamus Angela Merkel a birnin Berlin, Netanyahu ya yi gargadin cewa ci gaba da barin Iran na wataya a yankin Gabas ta Tsakiya zai iyar haifar da kwararar ‘yan gugun hijirar zuwa yankin Turai.

Yana dai Magana ne akan yarjejeniyar Nukiliyar da kasashen Nahiyar Turai suke kariya ne.

Daukacin manufofin ziyarar ta Fira Minista Netanyahu dai, sun ta’allaka ne kacokam ga kokarin da Isra’ila ke yi na dagula duk wata kariya da kasashen Turai ke bai wa yarjejeniyar Iran da kasar Amurka ta yi wa tawaye.

A takon farko na ziyarar kwanaki 3 da Netanyahu ke yi a yankin na Nahiyar turai da ya sauka a birnin Berlin na kasar Jamus, Fira Ministan ya fayyace wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel inda banbancin fahimta yake tsakaninsu dangane da yarjejeniyar ta Iran.

Ya ce wani abin da za su iya fahimta fa shi ne, yanzu Iran ta samu kafar girke dakarunta ne a sassan kasashen yankin gabas ta tsakiya daban daban da suka hada da Syria da Yemen, gashi kuma tana gangamin sauya tunanin musulmi ‘yan Sunni zuwa Shi’a, kuma a cewar Netanyahu wannan na iya kara rura wutar yakin da ake a yankin gabas ta tsakiya.

Isra'ila dai na so ta gamsar da kasashen Jamus da Faransa da Birtaniya, da su ne suka rattaba hannu ga yarjejeniyar Nukiliyar Iran a shekarar 2015.

A nata haujin kasar Iran ta gargadin kasashen yammacin Duniya da su daina yaudarar kansu a tunanin wai Iran na iya dakatar da aikin samar da makaman Nukiliya idan suka ci gaba da yi wa yarjejeniyar da ke tsakaninsu kariya, da kuma radadin Takunkumin karya tattalin arziki da aka saka mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.