Isa ga babban shafi
AMurka- korea

Wakilan Amurka da Koriya na ganawar karshe

Shugaba Trump da Shugaba Kim
Shugaba Trump da Shugaba Kim REUTERS/Kevin Lamarque & Korea Summit Press Pool
Zubin rubutu: Faruk Yabo | Azima Bashir Aminu
1 min

Manyan jami’an kasashen Amurka da Koriya ta Arewa na ganawar karshe domin share fagen taron shugabannin kasashen biyu da za su yi gobe talata a kasar Singapore.

Talla

Tuni shugaba Kim Jong Un da Donald Trump suka isa kasar ta Singapore domin shirin ganawar mai dimbin tarihi.

Shugabannin biyu sun isa kasar Singapore ne kwanaki biyu kamin zaman tattaunawar da za ta gudana a ranar Talata 12 ga watan Yuni.

Tun daga farko dai sai da aka fuskanci tirjiya da ta haifar da dari-darin yiyuwar ganawar ko akasin haka daga baya kuma masu shiga tsakanin kamar Fira Ministan kasar Japan Shinzo Abe suka sasanta lamarin.

Shugaba Kim Jong Un ne ya fara isa Singapore a jirgin Air China kirar 747 kafin daga bisani aka dauke shi da rakiyar jerin gwanon Motoci zuwa fadar Firaminista Lee Hsein Loong wanda ya jinjina masa da amsa gayyatar.

Rahotanni sun ce bayan fitar Kim daga Korea ta Arewa a safiyar jiya sai daya fara yada zango a kasar China kafin daga bisani ya zarce Singapore.

Shima dai shugaban kasar Amurka Donald Trump wanda ya isa Singapore da yammacin jiya ya zo ne kai tsaye bayan halartar taron kasashen G7 daga Canada indaaka ruwaito shi yana bayyana taron daganawar farko da za ta kai ga cimma zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.