Faransa-Wasanni

Faransa ta lashe kofin duniya

Rabon Faransa da lashe kofin duniyar tun a shekarar 1998, lokacin da faransar ta karbi bakoncin gasar kuma ta lashe abinta.
Rabon Faransa da lashe kofin duniyar tun a shekarar 1998, lokacin da faransar ta karbi bakoncin gasar kuma ta lashe abinta. REUTERS

Faransa ta fara bukukuwan lashe kofin duniya bayan kasar ta lallasa Croatia da ci 4 da 2 a wasan karshe da ya gudana a tsakaninsu a filin wasa na Luzinikh da ke Rasha. Bukukuwan nasarar lashe kofin na zuwa a dai dai lokacin da kasar ke bikin zagayowar ranar hadin kan ta da ya tabbata a shekarar 1790, bayan juyin juya halin shekarar 1789.

Talla

Antoine Griezman da Paul Pogba da Kyllian Mbappe ne suka jefawa Faransa kwallaye uku yayinda dan wasan Croatia Mario Mandzuki ya jefa kwallo guda a ragarsu.

A bangaren Croatia kuwa 'yan wasa irinsu Ivan Perisiic da Mario Mandzuki ne suka jefa musu kwallayensu biyu a raga.

Dama dai ana gudanar da bukukuwan na yau ne a Faransar bisa tsammanin kasar za ta lashe kofin duniya.

Bayan tashi daga filin wasan, an hango uwargidan shugaban Faransar Brigette Macron na taka rawa daga wurin da aka kebe musu don kallon wasan na yau wanda ya samu halartar shugaba Emmanuel Macron.

Rabon da Faransa ta dauki kofin duniya dai tun a shekarar 1998 zamanin su Zinadine Zidane wadanda suka dage shi lokacin da kasar ta karbi bakoncinsa.

Ko a wasan gab dana kusa dana karshe da ya gudana a makon jiya tsakanin Faransar da Belgium an hango shugaban kasar Emmanuel Macron a filin wasan wanda ya je don karawa 'yan wasan kasar kwarin gwiwa.

Jimillar sojoji 4,200, ababen hawa 220 da kuma jiragen yaki 100 ne suka gudanar da fareti a birnin Paris wanda aka shafe sama da sa'o'i biyu ana yi gabanin tafiyar shugaban kasar Rasha.

Domin gudanar da bukukuwan ranakun biyu a karshen makon nan, Faransar ta baza akalla ‘yan sanda 110,000 domin samar da tsaro a wuraren taruwar jama'a.

Daukar wannan gagarumin shirin samar da tsaro ya biyo bayan hare haren ta’addanci da aka samu a birnin Paris wadanda suka yi sanadiyar rasa rayukan mutane 246 a shekarar 2015.

Ministan cikin gida Gerard Collomb ya ce a birnin Paris kawai ‘yan sanda 12,000 za su shiga damarar ko ta kwana, tare da ma’aikatan kula da lafiya 3,000.

Shugaban Yan Sanda Michel Delpuech yace bukatar su ita ce ganin an kammala bukuwan ba tare da matsala ba.

Jami’in yace tun bayan shekarar 1998 da mutane sama da miliyan daya da rabi su kayi gangami a gaban fadar Elsees bayan Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya, basu sake ganin irin wannan gangamin jama’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.