Wasanni-Faransa

Tawagar Faransa ta samu kyakkyawar tarba a Paris

Tawagar 'yan kwallon Faransa lokacin da su ke isa birnin Paris bayan lashe kofin duniya daga Rasha.
Tawagar 'yan kwallon Faransa lokacin da su ke isa birnin Paris bayan lashe kofin duniya daga Rasha. REUTERS/Pascal Rossignol

Tawagar 'yan wasan kwallon kafar Faransa ta samu kyakkyawar tarba, yayinda dubban jamaá a kasar ta Faransa ke ci gaba da bukukuwan murnar nasarar da kasar ta samu na lashe gasar cin kofin duniya a jiya Lahadi.

Talla

Da misalin karfe 3 da mintina 45 ne tawagar ta Faransa ta sauka a babban filin jirgin saman da ke gab da birnin Paris kafin daga bisani a dauke su a manyan motoci zuwa fadar Elysee.

Kaftin din kungiyar Hugo Lloris ne ya fara sakkowa daga jirgin rike da kofin tare da rakiyar kociyansu Didier Deschamps kafin daga bisani sauran tawagar ‘yan wasan ta biyo bayansa.

An dai ga tawaga ta musamman na yiwa ‘yan wasan faretin ban girma, inda wani mazaunin birnin Paris Mallam Hashimu Umaru ya ce kwana suka yi suna gudanar da shagulgulan nasarar cikin kade kade da bushe bushe kan sake lashe gasar cin kofin duniya da suka yi, shekaru 20 bayan da suka lashe kofin gasar na farko.

Yayin murnar nasarar da suka samu kafin tasowarsu daga Rasha zuwa Faransa Paul Pogba daya daga cikin wadanda suka taka rawar gani ya bayyana cewa dole ne su yi farin ciki la'akari da yadda suka dawo da kofin bayan shekaru 20.

Tuni dai aka sada su da fadar Elysee inda suka sake ganawa da shugaba Emmanuel Macron wanda dama tun a jiyan tare da shi aka kalli wasan haka zalika tare da shi aka fara shagulgulan a Rasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.