Turai

Bakin haure na ci gaba da sa kai zuwa yankin Turai

Bakin haure a tasahar jiragen ruwa na Tarifa a kasar Spain
Bakin haure a tasahar jiragen ruwa na Tarifa a kasar Spain REUTERS/Jon Nazca

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin bakin dake tafiya Turai domin samun rayuwa mai inganci da suka isa kasar Spain bana ya zarce wadanda suka isa Italia.

Talla

Alkaluman da hukumar kula da yan gudun hijirar ta bayar, ya nuna cewar baki 50,872 suka tsallake kogin Mediteraniya zuwa Turai bana, adadin da ya zarce rabin wadanda aka samu a shekarar da ta gabata.

Kakakin hukumar, Joel Millman yace kamar yadda suka yi hasashe, yanzu haka baki 18,061 suka isa kasar Spain, sabanin 17,827 da suka isa Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.