Faransa-Macron

Za a fara bincike kan babban mai bai wa shugaba Macron tsaro

Alexandre Benalla babban mai bayar da tsaro ga shugaban Faransa Emmanuel Macron zai fuskanci bincike daga ofishin shigar da kara na kasar bayan wani faifan bidiyo da ya nuna yadda ya ke jibgar wani mai zanga-zanga.
Alexandre Benalla babban mai bayar da tsaro ga shugaban Faransa Emmanuel Macron zai fuskanci bincike daga ofishin shigar da kara na kasar bayan wani faifan bidiyo da ya nuna yadda ya ke jibgar wani mai zanga-zanga. Thibault Camus / POOL / AFP

Ofishin mai gabatar da kara a Faransa ya sanar da kaddamar da bincike kan wani babban jami’in tsaron shugaba Emmanuel Macron da aka dauka a faifan bidiyo yana dukan wani mai zanga zanga ranar 1 ga watan Mayu.Tuni faifan bidiyon ya janyo cece kuce a fadin kasar.

Talla

Jaridar Le Monde da ake wallafawa a birnin Paris ce ta fara buga hotan bidiyon wanda ke nuna jami’in tsaron shugaba Emmanuel Macron Alexandre Banalla na dukan wani mai zanga zanga da kuma taka shi da takalmi.

Shi dai Banalla wanda ba Dan sanda ba ne, ya samu izinin zuwa wurin zanga zangar ne domin ganin yadda 'yan Sanda za su gudanar da aikin su a tsakiyar birnin Paris ranar da aka samu matsalar.

Tuni fadar shugaba Macron ta ce an dakatar da Banalla na makwanni biyu bayan ganin bidiyon, kana an sauya masa wurin aiki daga aikin da yake ada na shiryawa shugaban kasa tsaro a wuarren da zai kai ziyara.

Bruno Roger-Petit, mai Magana da yawun fadar shugaban kasa ya ce sun dauki matakin ladabtar da jami’in wajen sauya masa wurin aiki.

Shugaba Emmanuel Macron ya ki cewa komi kan lamarin lokacin da manema labarai suka tambaye shi akai yau da ya kai wata ziyara, yayin da 'yan Majalisu daga Jam’iyyar adawa ke zargin cewar ana neman rufe maganar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.