Faransa-hakkin bil'adama

Dogarin Macron ya bayyana gaban alkali kan dukan mai zanga-zanga

Faifan Bidiyon na Farko ya nuna Benalla na dukan wani mai zanga-zanga yayinda bidiyo na biyu kuma wanda ya fi tayar da hankali ya nuna babban dogarin shugaban na Faransa na kokawa da wata mace har ya kai ta kasa ya kuma ci gaba da dukanta.
Faifan Bidiyon na Farko ya nuna Benalla na dukan wani mai zanga-zanga yayinda bidiyo na biyu kuma wanda ya fi tayar da hankali ya nuna babban dogarin shugaban na Faransa na kokawa da wata mace har ya kai ta kasa ya kuma ci gaba da dukanta. Tahar Bouhafs / AFP

Korarren Jami’in tsaron shugaban Faransa Emmanuel Macron, wato Alexandre Benalla ya gurfana a gaban alkali yau kan tuhumar da ake masa na lakadawa wani mai zanga zanga duka kamar yadda aka yada faifan bidiyon ta kafar sada zumunta.

Talla

Shugaba Emmanuel Macron ya ki cewa komai kan lamarin, amma kuma fadar shugaban ta sanar da korar sa daga aiki, yayin da Yan Majalisu daga bangaren adawa suka bukaci cikaken bayani kan lamarin.

Ofishin mai gabatar da kara yace wasu jami’an Yan Sanda guda 3 da suka baiwa Benalla bidiyon domin shirya kare kan sa daga tuhumar da ake masa, suma zasu amsa tambayoyi yau lahadi.

Tuni Majalisar wakilai da an Dattawa suka kafa kwamitin bincike kan lamarin, yayin da wasu daga cikin su ke zargin gwamnati da kokarin rufe maganar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.