Faransa

Macron zai yi garambawul saboda dukan mai zanga-zanga

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da babban dogarinsa, Alexandre Benalla
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da babban dogarinsa, Alexandre Benalla 路透社

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bada umarnin gudanar da garambawul a ofishinsa bayan ya amince cewar, fadarsa ta gaza wajen tinkarar badakalar da ta shafi babban dogarinsa da aka dauka a faifen bidiyo yana lakada wa wani mai zanga-zanga dukan tsiya a cikin watan Mayun da ya gabata.

Talla

Tuni mahukuntan Faransa suka fara gudanar da bibcike kan jami’in tsaron na Macron, Alexandre Benalla a karkashin wannan badakala da ta rura wutar siyasa a duk fadin kasar, in da Macron ke shan caccaka mafi zafi tun bayan darewarsa kan karagar mulki watanni 14 da suka gabata.

Shugaba Macron wanda tuni ya bada umarnin koran Benalla daga aiki, ya gana da kusoshin gwamnatinsa a ranar Lahadi don tattaunawa kan badakalar.

Shugaban ya ce, halin da dogarin ya nuna a ranar 1 ga watan Mayu, na da tayar da hankali, kuma ya ce, ba zai amince da kin hukunta duk wani jami’in da ke cikin tawagarsa ba matukar ya aika laifi.

An dai caccaki Macron ne kan jinkirinsa na a daukan mataki kan Benalla, yayin da ake zargin sa da yin rufa-rufa kan maganar.

Tuni Majalisar Wakilai da ta Datatwa suka jingine shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara domin gudanar da bincike kan lamarin.

Shi ma Ministan Cikin Gidan Kasar, Gererd Collomb zai bayyana a gaban Majalisun biyu a ranar Litinin don amsa tambayoyi kan wannan badakala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.