Faransa

Macron na fuskantar suka kan abin kunyar babban dogarinsa

Yanzu haka dai Ofishin shugaban kasar na halin tsaka mai wuya yayin da hankalin duniya ya karkata kanshi don jin irin hukuncin da zai zartas ga Benalla ko da dai dama tun farko ya sanar da dakatar da shi daga bakin aiki.
Yanzu haka dai Ofishin shugaban kasar na halin tsaka mai wuya yayin da hankalin duniya ya karkata kanshi don jin irin hukuncin da zai zartas ga Benalla ko da dai dama tun farko ya sanar da dakatar da shi daga bakin aiki. REUTERS/Francois Walschaerts

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ci gaba da fuskantar mummunar suka kan abin kunyar da tsohon babban dogarinsa Alexandre Benalla ya yi na dukan mai zanga-zanga bayan da ma’aikatar harkokin cikin gida da hukumar ‘yan sanda suka tsame hannunsu daga batun.

Talla

Matsin lambar ga shugaba Macron ya tsananta ne bayan da Ministan harkokin cikin gida na kasar da shugaban ‘yan sanda suka sanar da cewa ya rage Ofishinsa ya dau matakin da ya kamata kan faifan Bidiyon na Benalla.

Bangarorin biyu dai sun kare kan su ne gaban kwamitin binciken da Ofishin mai shigar da kara na birnin Paris ya kafa dangane da abin kungiyar na babban dogarin Macron Alexandre Benalla.

Yanzu haka dai Ofishin shugaban kasar na halin tsaka mai wuya yayin da hankalin duniya ya karkata kanshi don jin irin hukuncin da zai zartas ga Benalla ko da dai dama tun farko ya sanar da dakatar da shi daga bakin aiki.

Sai dai a bayanin da Benalla mai shekaru 26 ya yi a jiya Litinin, ya ce mutanen biyu da aka ganshi yana kokowa da su a wurin zanga-zangar mutane ne da ke d ahadarin gaske ga tarin jama’ar da ke wurin, matakin da ya sanya shi kokarin korarsu daga wajen inda har ma ya nemi taimakon ‘yan sanda.

Ministan cikin gidan Gerard Collomb da shugaban ‘yan sanda Michel Deluech sun ce sun kalli faifan bidiyon tare da mika sh i ga Ofishin shugaba Macron tun ranar 2 ga watan Mayu kwana guda bayan faruwarsu, inda suka bukaci ya dauki matakin da ya kamata kan Benalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.