Faransa-Birtaniya

Ganawar Emmanuel Macron da Theresa May

Ganawar Emmanuel Macron da Theresa May a Brégançon
Ganawar Emmanuel Macron da Theresa May a Brégançon Reuters

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a ranar farko ta hutun da ya fara a wannan juma’a, ya gana da firaministar Birtaniya Theresa May inda bayanai ke cewa sun tattauna kan batun ficewar Birtaniya daga gungun Tarayyar Turai.

Talla

An yi ganawar ce a Brégançon da kudu maso gabashin Faransa, inda shugaban ke hutunsa na karshen damina.

Ita ma Firaminista May, na wannan  ziyara a Faransa ce kwana daya bayan ta kammala nata hutun a kasar Italiya, to sai dai ba wasu cikakkun bayanai dangane da abin da mutanen biyu suka tattauna a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.