Turai

Tsananin zafi na ci gaba da karuwa a wasu sassan Turai

Sassan nahiyar turai na ci gaba da fuskantar matsanancin zafi, wanda da ya kai digiri 46 a ma’aunin zafin yanayi na Celsius a kasar Portugal, yayinda a wasu kasashen turan zafin ya zarta hakan.

Mutane da dama a yankin kudu maso gabashin kasar Spain, birnin Benidorm, yayin da suke kokarin rage radadin zafin yanayi da suke fama da shi, sakamakon dagawar ma'aunin zafi a wasu sassan turai. 2 ga watan Agusta, 2018.
Mutane da dama a yankin kudu maso gabashin kasar Spain, birnin Benidorm, yayin da suke kokarin rage radadin zafin yanayi da suke fama da shi, sakamakon dagawar ma'aunin zafi a wasu sassan turai. 2 ga watan Agusta, 2018. REUTERS/Heino Kalis
Talla

Tuni dai gwamnatin Portugal ta bayar da umarnin rufe duka wani wurin wasan yara da na shakatawa a birnin Lisbon tare da baiwa jama’a umarnin su kasance a gida.

A kasar Spain mutane uku suka rasa rayukansu, ciki harda da wani mai shekaru 78 da ke aiki a gonarsa a wannan mako.

A Vienna babban birnin Austria kuwa, tilas aka sanyawa karnukan da jami’an tsaro ke amfani da su wajen sintiri takalma, bayanda kwararru suka hasashen zafin zai karu daga matakin digiri 34 zuwa 50.

A kasar Holland kuwa tuni aka rufe wasu manyan tituna, sakamakon yadda tsananin zafin ya haddasa narkewar kwaltar da aka shimfida, sai kuma sare reshunan bishiyoyi da ke kumbura sun karyewa saboda zafin.

Rahoton wasu jami’ai ‘yan rajin kare muhalli da ake kira ‘Legambiente Association’ ya ce daga shekarar 200 zuwa yanzu akalla mutane dubu, bakwai da dari bakwai (7, 700) ne suka hallaka a birnin Lazio na kasar Italiya, sakamakon aukuwar irin wannan yanayi na zafi, a lokuta daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI