Isa ga babban shafi
Turai

Mutane da dama ne suka mutu a Girka

Gobarar dajin Girka
Gobarar dajin Girka FLYGREECEDRONE/via REUTERS
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya yi alkawarin ware dala milyan 500 domin sake fasalta hukumomin kula da wadanda bala’o’i suka shafa, biyo bayan wutar dajin da ta yi sanadiyyar asarar rayukan mutane 93.

Talla

Adadin mutanen da suka mutu a gobarar dajin Girka ya zarta 50, bayan da kungiyar bayar da agajin gaggawa ta RedCross ta kara gano gawar akalla mutane 26.

Hukumomi a kasar ta Girka sun sanar da mutuwar akalla mutane 24 tare da wasu 150 kuma da suka jikkata, sai dai bayan gano sauran gawakin mutanen 26 a kauyen Mati adadin ya karu zuwa 50.

Mai Magana da yawun gwamnatin Girka Dimitris Tzanakopoulos ya ce wutar wadda ta faro daga dazuka ta warwatsu ne zuwa wasu sassa na garuruwan da ke gab da dajin dama wuraren shakatawa da ke bakin teku.

A cewarsa galibin wadanda gobarar ta lahanta an same su ne ko dai a cikin gidajensu ko kuma a motoci yayin da wasu kuma gobara ta sanyasu fadawa teku.

Wannan ne karo na farko a tarihin kasar da aka samu asarar rayukan mutane masu tarin yawa sakamakon wutar daji a lokaci daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.