Isa ga babban shafi
Girka

Tallafin kudin da kasashen turai ke baiwa Girka ya kawo karshe

wani mai zanga zangar kyamar tsuke bakin aljihu a gaban majalisar dokokin kasar Girka a  Athènes, rana 11 Faware 2005.
wani mai zanga zangar kyamar tsuke bakin aljihu a gaban majalisar dokokin kasar Girka a Athènes, rana 11 Faware 2005. REUTERS/Yannis Behrakis
Zubin rubutu: Salissou Hamissou
Minti 2

Bayan share tsawon shekaru 10 a cikin matsalar tattalin arizikin da ta samu tallafin masu bada bashi na duniya har sau 8, a yau litanin 20 ga watan Ogusta, tallafin da hukumomin bayar da lamani ake baiwa kasar Girka ya kawo karshe.Albarkacin shirin tallafawa kasar kashi na uku, a yau masu bada ta tallafi na kasashen turai sun baiwa Girka tallafin karshe na Euro biliyan 289.

Talla

Masu bata tallafin na duniya, da suka hada da hukumar bayar da lamani ta duniya IMF, kungiyar tarayyar turai EU a yau litanin sun kawo karshen bashin da suke baiwa kasar, tare juwa shafin matsalar tattalin arzikin kasar ta Girka

Sakamakon karbar kashin karshe na kudaden tallafin da suka kai bilyan 289 na Euro, daga yanzu mahukumtan birnin Athènes, za su ja ruwa ne da ruwan cikinsu, ta fannain da ya shafi siyasar tattalin arzikin kasar ba tare da yi masu katsalandan ba

Sakamakon sauye sauyen tattalin arzikin da na tsuke bakin aljihun da ta samar, kasar ta Girka ta yi nasarar samun rarar 0,8%, a cikin kasafin kudinta, ta kuma dauki matakan zura ido kan yadda gwamnati ke kashe kudadeta tare da zaftare kaso mai yawa daga masu zuwa ritaya

sai dai har yanzu tattalin arizikin kasar na da rauni. Lura da yadda Kudaden cefane ke hawa da sauka, babu masu zuba jari da yawa, a yayin da kashi daya bisa uku na al’ummar kasar ke rayuwa da Euro 500 ne kacal a wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.