Turai

Macron zai sabunta kudirin yakar ra'ayin matsanancin kishin kasa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. ludovic MARIN / AFP

Yayin da ya rage watanni tara a gudanar da zaben ‘yan majalisun kungiyar tarayyar turai EU, shugaban Faransa Emmanuel Macron zai sabunta gabatar da kudurinsa na gannin an samar da kungiyar kasashen turan mai cikakken hadin kai.

Talla

Yukunrin na Macron ya zo ne a dai dai lokacin da ake samun wasu manyan kasashen duniya da ke rungumar, ra’ayin matsanancin kishi kasa da fifita kai.

A gobe Litinin a birnin Paris, ake sa ran shugaban na Faransa zai gabatar da jawabi ga jakadun kasashen turan na kungiyar EU.

Wasu daga cikin muhimman batutuwan da shugaba Macron zai tattauna a kai sun hada da, kasafin kudin bai daya na kasashen kungiyar EU, samar da rundunar sojin hadin gwiwar kasashen turai, da kuma cimma yarjejeniyar bai daya kan hanyar magance kwararar bakin haure zuwa nahiyar turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.