Turai

Emmanuel Macron zai gana da Angela Merkel a Marseille

Emmanuel Macron da Waziriyar Jamus Angela Merkel
Emmanuel Macron da Waziriyar Jamus Angela Merkel 路透社

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai karbi bakuncin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ranar juma’a mai zuwa a Marseille dake gabar ruwan Mediterranean, a yunkurin sa na sake fasalin kungiyar kasashen Turai.

Talla

Fadar shugaban Faransa tace taron shugabannin zai mayar da hankali ne kan kudin euro da batun baki haure da bangaren fasaha da kuma halin da duniya ke ciki.

Ganawar zata zo ne bayan Macron ya ziyarci Luxembourg ranar alhamis inda zai gana da Firaministan kasar da kuma takwarorin sa na Belguim da Netherlands.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.