Faransa

Macron na taka tsan-tsan kan zaben Minista

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cikin tsaka mai wuya bayan murabus din ministan muhalli
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na cikin tsaka mai wuya bayan murabus din ministan muhalli Lehtikuva/Markku Ulander via REUTERS

Bisa dukkan alamu, shugaban Faransa Emmanuel Macron na taka-tsan-tsan a kokarinsa na zaben wanda zai maye gurbin tsohon Ministan Muhalli da ya yi murabus a makon jiya, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawawar siyasa a kasar ganin cewa, murabus din na zuwa ne a dai dai lokacin da farin jinin Macron ke dakushewa.

Talla

Marabus din Nicolas Hulot da ya samu karbuwa a idon Faransawa na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaba Macron ke kokarin dawo da cikakken farin jininsa a kasar, yayin da yake ci gaba da fuskantar bore kan shirinsa na kawo sauyi a tsarin biyan kudaden haraji.

Ana sa ran nan da wani lokaci Macron ya sanar da wanda zai maye gurbin Hulot da ya zarce dukkanin Ministocin kasar wajen farin jini.

Tuni aka fitar da sunayen wadanda ake sa ran daya daga cikinsu zai maye gurbin Hulot bayan Daniel Cohn-Bendit, fitaccen mai gwagwarmayar kare muhalli ya ki amince wa da bukatar Macron ta nada shi Ministan Muhalli a karshen mako.

Rahotanni na cewa, murabus din Hulot zai tilasta wa Macron aiwatar da gagarumin garambawul a majalisar Ministocinsa gabanin wani taro da gwamnatinsa za ta gudanar a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.